Looking For Anything Specific?

Aisha Buhari Bataji Dadin Zanen Da Bulama Bukarti Yayi Ba Akan Auren Hanan Buhari

Auren Hanan Buhari

Bayan daura auren yar shugaban kasa Muhamadu Buhari wato Hanan Buhari da Angonta Muhd Turad wani dan jarida yayi wani zane wanda da alamu ahalin Shugaban basuji dadinsa ba, Mazauna Nigeria a shafukan sada zumunta sunyi tsokaci akan auren yar Muhammadu Buhari wanda wasu sun fadi alheri wasu kuma sabanin haka.

Matar Shugaban kasar wato Aisha Buhari ita da kanta ta wallafa hotunan shagalin auren yar tata a shafinta na instagram, Amma bayan daura auren da kwana daya zuwa biyu wani dan jarida mai suna Bulama Bukarti ya kwatanta yadda akayi auren a wani zane da yayi wanda daga baya abin yajawo ce ce kuce.

Zanen na Bulama ya nuna yadda yan Nigeria suke cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa daga sama kuma ga Aisha Buhari dauke da hoton yar ta Hanan da mijinta Turad sannan ya rubuta da turani: :At least you can enjoy the pictures, wato: "Kwa Iya Kallon Hotunan Bikin" bayan wannan zane daga baya mai magana da yawun Aisha Buhari yafito ya bayyana rashin jin dadinsu akan wannan zane.

zanen bulama bukarti

Aliyu Abdullahi mai magana a matsayin Aisha yace Zanen da Bulama yayi babu adalci aiki, Domin halin da yan Nigeria suke ciki bashi alaka da auren Hanan Buhari don haka wannan abu bai dace ba kwata kwata, Yaci gaba da cewa ya yan kowane Shugaban kasa suna dadamar yin aure idan lokaci yayi koda ana cikin yanayi na dadi ko akasin haka.

Wani mai tsokaci a shafukan sada zumunta ya bayyan ra'yinsa da cewa bai kamata ayi wannan aure ba yanzu, A rin halin da dan Nigeria yake ciki kuma yaga ana shagalin auren yan Shugaban kasa Muhammadu Buhari dole ransa yabaci, Inji Sani Musa.

Post a Comment

0 Comments