Looking For Anything Specific?

Sakon Abubakar Shekau Akan Wanda Yayiwa Annabi Muhammadu Batanci a Kano


Tun bayan hukuncin kisa da wata kotu a kano ta yanke akan wani mawakin kasida mai suna Yahaya Aminu Sharif wanda yayi kalaman batanci ga Manzon Allah lamarin yajawo cece kuce musamman a shafukan sada zumanta, Mutane dadama suna ganin hukuncin yayi dadai musamman idan aka duba da koyarwar addinin musulunci ga duk wanda yazagi Annabi Muhammadu hukuncinsa kisa ne.


Sai dai wasu kungiyoyi sun soki hukuncin da kotun ta yanke inda suka ce bai kamata a kashe wannan mawaki ba, Acikin masu tofa albarkacin bakinsu a wannan lamari har da shugaban kungiyar Boko Haram wato Abubukar Shekau inda yazargi dukkan musulaman Najeriya da aikata laifin batanci.


Abubakar Shekau yayi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga masu cewa ya  domin raddi ga masu ganin cewa hukuncin kisan da aka yankewa Yahaya Sharif Aminu yayi tsauri, Sanannen lauyan nan dake garin Kano wato Bulama Bukarti shi ya wallafa kalaman da Shekau din yafada a shafinsa na Twitter kamar haka:


Labarin da ake yadawa cewa Shekau ya soki batun hukuncin kashe Yahaya Aminu Sharif ba gaskiya bane, asali ma Shekau ya goyi bayan hukuncin kisan ne. Bugu da kari Abubakar Shekau ya bada shawarar a gaggauta kaddamar da hukuncin kuma a janye masa damar daukaka kara.


Sannan Abubakar Shekau yazargi dukkan Musulman Najeriya da aikata babban laifi wajen goyon bayan wanda ya aikata batanci ga Annabi Muhammadu, Kamar yadda Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Post a Comment

0 Comments