Looking For Anything Specific?

Mutuwar Buruji Kashamu: Wasikar Da Obasanjo Ya Rubuta Tabar Baya Da Kura

Buruji Kashamu Death

Biyo bayan mutuwar sanatan Ogun Buruji Kashamu da alama wata wasika da tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya rubuta domin jimamin mutuwar sanatan ta jawo cece kuce, Obasanjo ya wallafa rubutun domin bayyana alhini da kuma jajanta Mutuwar Buruji Kashamu sai dai mutane dadama suna ganin abin daya rubuta kamar cin mutunci ne.


Buruji Kashamu ya rasu ranar asabar 8 ga watan  Agusta 2020 wanda bayanai suka nuna cewa ya mutu ne sanadin cutur korona a wani asibiti dake garin Lagos, Abokin sanatan shine ya tabbatar da labarin kamar yadda manema labarai suka rawaito.


A wasikar da Obasanjo ya rubuta yace: " A lokacin da Buruji Kashamu yake da rai yayi amfani da karfin doka da kuma na siyasa domin kaucewa zargin da ake masa na laifukan daya aikata a qasar Nigeria da kuma wadansu kasashen ketare.


"Amma kuma babu wata doka ta siyasa ko al'ada ko kuma wani yanayi na rashin lafiya da zata hana mutuwa daukar ran Kashamu a lokacin da ubangiji ya kaddara lokacinsa yayi, A karshe Obasanjo yace Allah ya gafarta masa zunubansa kuma Allah yasashi a Aljannah, iyalansa kuma Allah yabasu hakurin wannan rashi, Inji Obasanjo.


Wadannan bayanai da tsohon shugaban yayi sun jawo cece kuce a shafukan sada zumanta musamman Twitter inda mutane dadama suka soki wadannan kalamai suna ganin ba dace Obasanjo ya fadesu ba, A wani bangare kuma manema labarai sun rawito cewa mai magana da yawun Obasanjo wato Adeyemi yace: Obasanjo yana da ra'ayinsa akan kowane irin mutum wanda yake mace ko wanda yake raye.


Sannan yace masu sukar Obasanjo don ya rubuta wannan wasika a shafukan sada zumunta suna da yancin badin bakinsu kuma Olusegun Obasanjo baya dana sanin rubuta wannan wasika.


Post a Comment

0 Comments