Looking For Anything Specific?

Harin Boko Haram: Zulum Yazargi Manyan Sojoji Dayin Zagon Kasa Bayan Kai Masa Hari Da Yan Ta'adda Sukayi

Harin Boko Haram: Zulum Yazargi Manyan Sojoji Dayin Zagon Kasa Bayan Kai Masa Hari Da Yan Ta'adda SukayiHarin Boko Haram: Zulum Yazargi Manyan Sojoji Dayin Zagon Kasa Bayan Kai Masa Hari Da Yan Ta'adda Sukayi
Harin Boko Haram


Wani abin mamaki yafaru bayan gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zulum yasha da kyar a wani hari da yan ta'adda suka kai masa wanda ake zargin yan Boko Haram ne. Lamarin dai yajawo cece kuce da kuma sanya fargaba a zukatan talakawa musamman wanda suke fama da rashin tsaro a jahohinsu, Abin da masu hangen nesu suke fada shine tunda aka kaiwa Gwamna hari to ina ga talaka.


Lamarin yafaru ne a lokacin da Zulum yatafi wani zagaye dashi da jami'ansa domin duba wani yanki dake jahar Maiduguri, A wani video mai tsawon Minti uku anga yadda ake barin wuta tsakanin Jami'an tsaron Zulum da kuma wasu ta'dda wanda kusan da kyar Gwamna Zulum yashiga cikin mota saboda ruwan harsashe da akayi tayi.


A wata hira da Zulum yayi da manema labarai bayan faruwar lamarin yace Jami'an tsaro suna zagon kasa sosai wajen kawar da yan ta'adda da ta'addanci a Nigeria, Babagana Zulum yace bazai iya yin shiru yana gani ana kashe mutane babu gaira babu dalili ba, Saboda kafin yahau mulki rantsuwa yayi tsakaninsa da Allah akan zai kare al'umar jahar Borno.


Zulum yace akwai bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lura da cewa wannan zagon kasa da yake faruwa a lamarin tsaro yafi kowane abu hadari kuma hakan shi yahana a shawo kan matsalar da take faruwa sama da shekara goma.


Sojoji sun dora alhakin kaiwa Zulum hari kan kungiyar Boko Haram sai dai kuma shi Gwamnan Jahar Borno yana ganin cewa da sanin sojojin irin wadannan abubuwa suke faruwa. Wannan abu yana faruwa ne a lokaci da Jahar Borno ke kara samun hare haren yan ta'adda wanda kwanan nan aka kai wani hari wanda yayi sanadiyar kashe mutum 15 ciki har da yara kanana a yankin iyakar kasar da kamaru.


Zulum bashi ne mutum na farko daya bayyana cewa akwai zagon kasa a lamarin tsaron Nigeria ba, Sai dai har yanzu bayan duk korafe korafe da akeyi kusan za a iya cewa babu wani chanji wajen kawo karshen ta'addanci a kasar Nigeria.

Post a Comment

0 Comments