Looking For Anything Specific?

Fashewar Beirut: Wani Abin Fashewa Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 100 Da Raunata Sama Da 4000 a Lebanon

Wani Abin Fashewa Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 100 Da Raunata Sama Da 4000 a Lebanon


Wani abu
wanda za a iya kwatantashi da Bom ko gurneti yayi mummunar barna a birnin Beirut dake kasar Lebanon, Wannan lamari yafaru ne ranar Talata inda wata fashewa ta kusa sanadiyar shafe Beirut saboda tsananin karfinta. Wanda har zuwa yanzu ana ta kokarin zakulo mutane wanda gini ya rufta a kansu wasu a mace wasu kuma da manyan raunuka.


Karfin fashewar ya girgiza gaba daya birnin Beirut kuma ya lalata manyan da kananan gidaje dake nesa da inda fashewar ta wakana, Tsananin karfin fashewar ne yasa gidajen dake nisan kilomitoci daga inda abin yafaru sai da suka lalace.


Shugaban kasar Lebanon Michal Aoun yace akwai wani sinadarin Ammonium Nitrate da ake hada takin zamani dashi da kuma abubuwan fashewa wanda yawansa yaka ton 2,750 wanda aka ajiye tsawon shekara shida shine yayi sanadiyar fashewar da tayi mummunar barna. Shugaba Michal Aoun dashi da ministoci zasuyi zama ranar laraba sannan yasanya dokar tabaci har tsawon sati biyu.


A yanzu haka dai a kasar Lebanon ana zaman makoki sakamakon mutuwar sama da mutum 100 da aka rasa a Beirut, Za a shafe tsawon kwana uku ana zaman makoki a duk fadin kasar tun daga ranar Laraba.


Ministan Harkokin cikin gida na kasar Lebanon yace sun gano cewa wani sinadarin Ammonium Nitrate da aka ajiye a tashar jirgin ruwa yayi sanadiyar wannan fashewa, Minsta Hassan Diab yace za a hukunta wanda sukayi sakacin faruwar wannan mummunar fashewa.


Baza a mu kyale wannan lamari yawuce haka bamu dauki mataki ba, Dukkanin wadanda sukayi gangancin faruwar wannan fashewa zasu gane kurensu. Wannan alkawari ne muka dauka ga wadanda suka rasa rayukansu da wanda suka samu raunka cewa lallai zamu dauki mataki. Inji Minista Hassan Diab

Post a Comment

0 Comments