Looking For Anything Specific?

Allah Yayiwa Jarumar Kannywood Fadila Muhammad 'HUBBI' Rasuwa Yanzu Yanzu

Allah Yayiwa Jarumar Kannywood Fadila Muhammad 'HUBBI' Rasuwa Yanzu Yanzu

Inna Lillahi Wainna Ilahi Rajiun, Allah yayiwa daya daga cikin jaruman Kannywood mata rasuwa Ummi Lolipop wasu kuma sun santa da Fadila Muhammad wace tafito a shahararren film din hausa HUBBI da sauran finai finai, Jarumar ta rasu ranar Juma a 28 ga watan Agusta 2020 wanda wata majiyar tace ta rasu ne cikin dare.

Mutuwar Fadila Muhammad tazo kusan bazata domin babu wata majiya data bayyana cewa Jarumar bata da lafia ko wani abu mai kama da haka, Kusan za a iya cewa Fadila Muhammad bata fina finan Hausa a yanzu domin an dade ba a ganta a wani sabon film din Kannywood ba.

Yan Kannywood maza da mata rasuwar Jarumar yayi matukar jefasu cikin alhini da jimami, Yan wasan Hausan dadama sun bayyana ta'aziyar su a shafukan su na Instagram da kuma jajantawa yan uwan Fadila Muhammad na rashin da sukayi.

Da safiyar ranar asabar ne akayi Jana'izar Jaruma Fadila Muhammad a gidan su kuma abokan sana'arta dadama sun halarci wajen sallar jana'izar da kuma rakiyar Fadila zuwa makwancinta, Allah yajikanta da rahama idan tamu tazo Allah kasa mu cika da Imani.

Post a Comment

0 Comments