Looking For Anything Specific?

Yadda Zaka Duba Number Alayin MTN, Airtel, Glo, Da 9Mobile Cikin Sauki

Yadda Zaka Duba Number Alayin MTN, Airtel, Glo, Da 9Mobile Cikin Sauki
Yadda Zaka Duba Number Alayin MTN, Airtel, Glo, Da 9Mobile Cikin Sauki

Miliyoyin mutane ne suke amfani da layukan kiran waya a Nigeria, Sai dai mafi yawan masu amfani da Sim Cards basusan yadda zasu duba lambar layin dasuke amfani dashi ba. Akwai layuka masu yawan mutane kamar irinsu: MTN, Airtel, Glo, 9Mobile da sauransu, Abin daza mukawo yau shine Yadda Zaka Duba Number Alayin MTN, Airtel, Glo, Da 9Mobile Cikin Sauki muna fatan zaku karanta wannnan rubutu har zuwa karshe.


A wasu loquta yana faruwa wata bukata ta kama mutum domin duba lambar layin wayar dayake amfani dashi kuma baisan yadda zai duba lambar layin ba, Sannan yawancin sabbin layuka yanzu suna zuwa batare da lambar layin ajikin bangon layin ba. Saboda irin wadannan dalilai yakamata kasan yadda ake duba lambar layin waya wanda yau zamuyi bayani akan Yadda Zaka Duba Number Alayin MTN, Airtel, Glo, Da 9Mobile Cikin Sauki.


Yadda Zaka Duba Lambar Layin MTN Da Hanyoyi Guda 2 - Check MTN Number 

Akwai hanyoyi dayawa dazaka duba lambar layin MTN wanda aciki zamu kawo guda biyu wanda babu shakka wajen yin amfani da wadannan hanyoyi domin suna aiki.

*1 Mataki Nafarko

Zaka danna *123# sannan kadanna 1 sannan kasake danna 1 zakaga lambar layinka ta bayyana. Zakuma ka iya yin abin a lokaci daya idan kadanna *123*1*1# nan take zakaga lambar layin.

*2 Mataki Nabiyu

Zaka iya duba lambar layin MTN da wannan mataki wanda yafi wancan sauki, Zakaga lambarka ta MTN idan kadanna *663# wani allo zai bayyana dauke da lambar layin.

Wadannan mataki guda biyu kowanne yana aiki wajen duba MTN Number dafatan zaka gwada.


Yadda Zaka Duba Lambar Layin Airtel Da Hanyoyi Daban - Daban - Check Airtel Number 

Wajen duba lambar layin Airtel akwai matakai dayawa ba kamar na layin MTN ba, Sai dai wasu loquta wata hanyar tana iya dena aiki kokuma kaga tana daukar lokaci kafin tanuna maka lambar layinka. Saboda haka zamu kawo hanyoyi mabanbanta wanda zamu ware hanyoyin da sukafi inganci acikinsu.

*1 Mataki Nafarko

Zaka danna *121# idan kashiga zakaga jeri sai kazabi 3 idan kashiga zakaga wani jerin daban, Aciki zakaga inda aka rubuta My Number yana kan lamba 4 idan kashiga zakaga lambar layinka na Airtel kokuma atakaice kadanna *121*3*4# yawadatar. Wannan hanya itace tafi inganci kuma babu shakku acikinta wajen Duba Airtel Number.


*2 Mataki Nabiyu

Wannan mataki yana da hanyoyi daban daban na duba Airtel Number amma babu tabbas duk wadannan matakai zasuyi aiki, Don haka zaka iya gwadawa ida kasamu wadda tayimaka aiki shikenan. Wadanna lambobi daza mukawo akasa kowace ana iya duba lambar layin Airtel da ita:

*282#
*140*1600#
*140*175#
*141*123#
*400*2*1*10#

Da wadannan hanyoyi da muka kawo zaku iya duba lambar layinku na Airtel cikin sauki, Sai kuzabi hanyar dazaku gwada.


Yadda Zaka Duba Lambar Layin Glo Da Hanyoyi Guda Biyu - Check Glo Number 

Domin duba lambar layin Glo shima yana bukatar kasan hanyoyi da ka'idodinsa, Hanya biyu zamu kawo dazaka iya duba Glo Number dasu.

*1 Mataki Nafarko

Idan kana so kasan lambar layinka na Glo zaka kira wadannan lambobi 1244 sannan sai kasaurara zakaji andaga kiran kada kayi magana zakaji ana gaya maka lambar layin dakayi kiran dashi, Wannan kira kyauta ne kada kayi tsammanin za a chajeka kudi.

*1 Mataki Nabiyu

Sannan ana iya duba lambar layin Glo ta hanyar danna lambobi kamar dai MTN da Airtel. Wannan hanya tafi sauki domin basai kasha wahala kira da kuma saurara ba, Kawai zaka danna wadannan lambobi *135*8# nan take zakaga lambar layinka na Glo.


Yadda Zaka Duba Lambar Layin 9Mobile Da Hanya Guda Daya - Check 9Mobile Number

Hanya dayace zamu kawo wanda zaka iya duba lambar layin 9Mobile da ita, Idan kana so kasan 9Mobile Number wanda kake amfani dashi sai kadanna *248# zakaga lambar layinka nan take.


Wadannan sune hanyoyi da matakai dazaka iya duba lambar layin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile da wayarka. Muna fatan wannan rubutu zai amfaneku kuma idan akwai abin daba kugane ba zaku iya yin comments akasan wannan post zamu amsa muku tambayoyinka akowane lokaci. Idan wannan rubutu yayi maka amfani kayi kokari katurashi zuwa wasu gurare, Mungode.

Post a Comment

0 Comments