Looking For Anything Specific?

Hajj 2020: Abubuwa Guda Biyar Daya Kamata Kayi Domin Samun Falalar Ranar Hawan Arafa

Hajj 2020: Abubuwa Guda Biyar Daya Kamata Kayi Domin Samun Falalar Ranar Hawan Arafa


Kamar yadda yake gudana a qasar Saudiya mahajjata suna can suna sauke farali domin yin aikin hajji na Shekarar 2020 wanda yayi daidai da ga 9 ga watan Dhul Hijjah wato Hijra 1441,  Ana gabatar da aikin hajjin ne a yanayin na annobar cutar korona wanda tasa kusan duk wanda suke zuwa aikin hajjin bana basu samu damar zuwa ba. 


Rana Arafa rana ce mai muhimmanci kuma tana cikin ka'idodi na aikin hajji, Acikin wannnan rana ce Alhazai suke taruwa a wani fili da ake kira Filin Arafa dake garin Makkah daga bayan kaucewar rana daga tsakiyar sama zuwa faduwar ranar wanda hakan yana daya daga cikin sharadai na aikin Hajji.


Ga jerin abubuwa guda biyar na falalar ranar Arafa, Wannan sun hada da:

1. A rana irin ta Arafa ne lokacin Hajjin bankwana a zamanin Ma'aiki Annabi Muhammadu (S.A.W) Allah mai girma yagama saukar da duk wani hukunce hukunce daya shafi musulunci, Domin tun daga wannan rana ba a kara saukar da wata ayar Qu'ani ba.


Wannan shiyasa Sayyadina Umar yake cewa Muhimmancin ranar Arafa da ace Yahudawa ne suke da wannan rana to da biki zasu nayi duk lokacin da ranar ta zagayo, Kuma bayan wannan rana ce da kwana 81 Allah yakarbi rayuwar Annabi Muhammadu (S.A.W).


2. Samun yin addu'a a ranar Arafa itace tafi daraja na duk wata addu'a a fadin duniya, Annabi Muhammdu yace: Addu'a mafi daraja itace addu'a a ranar Arafa.


3. Sannan a ranar Arafa ne Allah yake yawanta yanta bayinsa daga shiga wuta, Imam muslim yarawaito cewa: Annabi Muhammdu yana cewa: Babu wata da Allah yake yawanta yanta bayinsa kamar ranar Arafa.


4. Wani abu mai muhimmanci shine Azumi Ranar Arafa, Akwai wani Hadisi da aka rawaito Annabi Muhammdu yana cewa: Azumin ranar Arafa yana wanke zunubi na shekarar data gabata da kuma shekara mai zuwa, Imam Muslim ne yarawaito wannan hadisi.


5. Sannan Allah yana alfahari da Alhazai wanda suka halarci Arafa a wannan rana, Imam Ahmad yarawaito cewa a wani hadisi: Annabi Muhammadu yana cewa "Allah yana alfahari da mazauna sama da wadanda suka halarci filin Arafa. 

Allah Kasa Mudace Alkhairan Wannan Rana Mai Daraja.

Post a Comment

0 Comments