Looking For Anything Specific?

Glo Yakata: Yadda Zaka More Tsarin Glo Yakata


Mafi yawan masu amfani da layin glo basu san yadda zasu shiga tsarin glo yakata su more saukin yin browsing da kuma kiran waya ba, Amma idan kana biye damu yau zaka san yadda ake shiga tsarin glo yakata da kuma yadda zakayi amfani dashi.


Glo Yakata wani tsarin layin glo ne wanda yazo da babbar garabasa ga masu amfani da Internet ko kuma yawan kiran waya, Wani tsari yana bada Bonus na kaso 125 aduk lokacin da kasa katin glo.


Yawan katin glo da kasa yawan garabasar daza kasamu, Wato atakice tsarin yana amfani da adadin kudin daka saka shine adadin Bonus dinka. Idan kasaka katin N500 zaka samu 2.4GB da kuma N1700 na kiran waya.


Yadda Zaka Shiga Tsarin Glo Yakata

Idan Kana son shiga wannan tsari zaka iya batare da bata lokaci ba, Zaka iya shiga da tsohon layin glo shi kuma sabon layin glo dama yana zuwa cikin tsarin Glo Yakata NE. Domin shiga wannan tsarin Yakata sai kadanna *220# akan wayarka nan da nana zaka shiga wannan tsari, Idan kana so kaduba cewa kashiga ko baka shiga ba zaka iya danna *100# Glo zasu nuna maka tsarin dakake ciki.


Idan kana son duba data balance na Glo Yakata zaka iya danna *127*0# zakaga adadi data daka samu dakuma bonus da suka ba, Wannan bayani akan yadda ake amfani da tsarin glo Yakata atakaice dafatan kunji dadin wannan rubutu, Mungode.

Post a Comment

0 Comments